Sunday 14 February 2016

Dangin Mijina Episode 3 February 14 2016

Read The previous episode click here


Nace Allah sutura wallahi banyi laifiba nahau bada hakuri anan nurse din ta ban magani kasancewar weekend ne ranar kuma ba malamai yasa bawani staff dayasani.muka koma hostel dakyar su furyad suka matsamin naci abinci gashi ranar wai anyiwa ss2 laifi akataramu a field din makarantan. Aka ware ss1 daban aka bamu purnishment dinmu. Wata sister Y Amina muhammed muna shiri sosai da ita. Tace majidadi kekan aibaki da lafiya jeki daki ki kwanta nan namike na je daki nakwanta kenan har bacci yafara kwasana kawai naji saukan duka wani irin firgit nayi saidatamin sha biyu a jere, tadaga bulalan ta kundumamin wani ashar meya kawoki hostel ban iyacewa komai ba sai wani hawaye dayake fitamin nace sister aisha wallahi sister Y Amina ne tace nadawo, tace dakeda Y aminan malapar ubanku!!auxubillah nace dakarfi.

  Wani irin kara tasaka tafara duka na baji bagani saida sandunan suka karye dorinan ya mokade anan metron tashigo ta finciketa ta wurgata gefe. Aisha dama bakida hanksli? Me yarinyan tamiki dazaki mata duka har haka? Keda principal gobe Allah yakaimu tafice matron kuma tajani takaini kan gado, alokacin andawo daga purnishment din bawanda bai tausayaminba mate dinmu sai zuwa suke suna gaysheni nayi narau narau ko ina a kumbure, wani irin zazzabi yarufeni haka narinka jinya har ran monday. Dayake English mukedashi first period Ahmed G nashigowa yalura bananan a zatonsa ko lattin danasabayine anma dayaga yagama first period baiganniba. Yace wasu zafyra ina Mayah? dama Mayah yake cemin sukayi narai narai da ido sai yan ajin sukace batada lafiya. Meya sameta? Anan kowa yayi tsit kowa na tsoron fada daga baya azo aci kaniyanshi. Ya buga musu tsawa badaku nakeba? sai furyad tace sister head girl ne tamata duka. Wani irin razana yayi what!!? metayi? sukayi tsit nanma. Yace furyad tatashi tadaukoni takaini dispensary shikuma yaje gun, anan nurse din tabashi labari meya faru. Yaharzuka sosai tunda take dashi bata taba ganin bacin ransaba, adaidai nan muka shigo yana ganina yace ashhaaa. Nurse shine ba’a mata treatment ba! Zafyra tace a a. Tamata wani dukan aka karayi.yace kuzauna anan amata duk abinda yadace. Yakallen yayi murmushin dole wanda nasan a dole yayi sannu mayah.
 Allah yakara sauki yafice bayan angama wankemun ciwukan ina zaune kawai naga kaf ss2 wanda suka min duka dawanda suka sabaki dawanda suka sa hannu sunyi layi a kofan dispensary, yaleko mayah fitonan. Na fita ina kishingida gatanan kufara. Abun yadauremin kai daya bayan daya suka taso sunaban hakuri, nayi shiru a zuciyata nace don Allah ahmed G karufamin asiri kar nakoma hostel suci kaniya na. Ina wannan tunanin saiga aisha alkali itama tazota taban hakuri, sannan tajuya wani fincika yamata ya gaggaura mata mari. Dan ubanki haka mukayi dake? Alkawarin damukayi dake kenan? Zaki zaga kici amana? dama haka kike? to a kunnen umma. Wani irin kuka tasaka haba big bross kayi hakuri mana abun yadaure min kai matuka, dama akwai alaka tsakanin aisha alka da ahmed G?
Yasa sukayi layi tundaga admin block yakesasu tsallen kwado har dinning hall. Yana binsu da bulala, sunyi narai narai kam balaifi duk malamin dayazo yamishi magana baya ko kallonsu donhaka saisu juya batare da sunce komaiba. Bayan sungama tsallen kwadon. Yace yau anhutar damasu aikin makaranta. Haka yasa suka share classes, hostel, da kuma admin block. Yasa suka wanke bayan gidan teachers ranar har karfe biyar suka kai suna aiki nikuwa yafita yakawo abinci yakawomana mukaci mukayi nak hankalina a kwance.furyad kuwa duk tabi ta tsure wai kar a koma hostel sumana duka. Makaranta kuwa kowa sai yadada tabbatar da zarginsa akan cewa muna soyayya da ahmed g inbahaka ba wannan hukunci ai tsauri gareta. Bayan yagama sasu aikin yakirani sannan yace gata agabanku barin rantse muku kuji, wallahi tallahi ko dauko cokali kuka sata zaku wahala ahannuna. Inada sunayenku ba ita zata fadamunba, securities nasaka donhaka saiku kiyaye. Sannan dukka masu post acikinku daga yau kutabbata kunyi ban kwana dashi zansa principal gobe yacireku. Ko bacemun kowaccensu cikin sanyin jiki suka mike, aisha alka ce tazauna. yace tazo tataho tare da durkusawa, yaya kayi hakuri bazan karaba.
   Na kalleshi shima kallon nawa yake sannan yace mayah? Wannan kanwatace , cousin ditace  na gyada kai sannan yace tatashi tatafi. Bayan tafiyanta ne yake cemin babanta da babana uwarsu daya ubansu daya. A hatsarin jirgi babanta da mamanta suka mutu, lokacin suna dawowa daga aikin hajj hakan yasa take zaune a gidanmu har yui. Itada kanwata Itakuma tana FGGC Bansan meyake damuntaba. Tana sona anma ni bana sonta, ni akwai wacce nakeso tun randa nafara ganinita nakesonta anma ban gayamata bane. Sabidah ina ganin kaman tayi karam!. Nayi kafaii ina kallonshi yau ahmed G ne yake cemin ‘he’s in love’. Lallai nayarda duk jida kai na namiji a kasan takalmin mace zai aje. Haka mukadanyi tadi sannan yace natafi masallaci a kishingide natafi, a masallaci ne muka hadu dasu zafyra muna zaune muna dan tadi sai aka dauke wuta. Aka tada gen. Shima yadauke muna jirane ayi isha’i. Sai gasu aisha alka da yan kwanansu sunzo mu muna ganesu sukuma kasancewar a duhu yasa su basu ganmuba anma mu mungansu.bayan sun idar sai dayan tacewa aisha alka, wai ni dama yasan kinasonshine? wallahi yau anraina mana hankali ai wannan zaisa yarinyan ta rainamu, aisha alka tace barshi. Wai adole ita yakeson aura. Wancan hutun komawana naji yana magana cewa akwai wata dalibarsa yanaso anma bai gayamataba. Dayan tace hehe. Aikuwa idan aka aureta kin kade. Aishan alkan tace kokuma ta kadeba! Angayamata dangin miji wasane! ? Sukayi shewa sannan sukacigaba. Nikan ganin antashi sallah ishai yasa muka mike. Muna idarwa muka wuce prep.
Awashegarin bansan yadda ahmed G. Yayi da principal ba. Aka tarasu a assembly aka kwace green dankwali aka bawa wasu. Principal din yayita korafi akan muguntan da prefect din sukayi. Wata sister Y amina muhammed akabawa head girl. Mukam munji dadi koba komai munhuta tunda muna mutunci da ita.








Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment